الأحد، 18 أغسطس 2019

TSAYUWA A KAN TAFARKI


Hudubar Masallacin Annabi na sheikh Husain Al- Ashaikh 15-12-1440AH

Hudubar Farko
Ya ku musulmai!
Na daga cikin ni'imar Allah a gare mu da ya shiryar da mu ga wannan Addini,ya kuma sanya mu musulmai: (Ku tuna ni'imar Allah a gare ku da Alkawari mai karfi da ya yi da ku a yayin da kuka ce mun ji mun bi, ku ji tsoron Allah, lalle Allah masani ne ga abin da ke cikin zukata.)
 Ya ku wadanda Allah ya musu ni'ima da kammala hajjinsu, ya wadanda aka musu baiwan ayyukan da'a a lokutan alheri to ku gode wa Allah Mai tsarki ku tsayu a kan lazimtar addininSa. Da shari'ar sa da nisatar saba mishi  da kuma ketare iyakoki Allah madaukakin sarki ya ce ;-  ( Sai  ka daidaita  kamar yadda aka umurce ka kai da wadan da suka  tuba  tare da kai  kuma ba  masu kyatara haddi ba lallai shi mai gani ne ga abin da kuke aikatawa )
(An karbo daga Abu Sufyan Dan Abdallah As-sakafi Allah ya kara yarda a gare shi ya ce ;- Na ce ya manzon Allah  ka fada mini wani fadi a musulunci wanda ba sai na tambayi wanin ka a bayan ka  ba sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce;- '' ka ce na yi imani da Allah sannan ka daidaita  ) muslim ne ya rawaito
 Lallai aikin musulmi a wannan rayuwa shi ne daidaituwa akan  kadaita Allah mai tsarki da daukaka  da dayanta bauta gaba daya a gare shi , shi kadai  adu'a ne, roko ne, fata ne , tsoro ne  da kuma kwadayi da firgici  fadi da aiki  cikin da waje  a bayyane da boye  Allah madaukakin sarki ya ce :- (ka ce lallai ne sallata  da ibada na  da rayuwata da mutuwa ta na Allah ne Ubangijin talikai babu abokin tarayya gare shi kuma da wancan aka umarce ni  kuma ni ne farkon masu sallamawa )    
Lallai ita ce daidaito wadda take sanya ka  mai tsananin kauna  ga mahaliccin ka   tsarki ya tabbata a gare shi  tare da cikan kankan da kai a gare shi wanda sha'anin sa ya buwaya  da girmamawa,  lallai girmamawa ne wanda ya kunshi kadaita Allah  wanda  yabon sa ya girmama sunayen sa sun tsarkaka  da abin da ya kebanta da shi , mai tsarki na daga  rububiyya  da uluhiyya da sunaye da siffofi  Allah madaukakin  sarki ya ce ;- (ku bi abin da aka saukar zuwa  gare ku daga Ubangijin ku , kuma kada ku rinka bin wasu majibinta baicin sa)
(Kuma (ance mini) ka tsyar da fuskarka  ga addini kana karkata zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga masu shirka   kuma kada ka kirayi baicin Allah abinda baya anfaninka kuma baya cutarka to idan ka aikata haka saannan lalle kai a lokacin kana daga masu zalunci kuma idan Allah ya shafeka da wata cuta to ba mai yaye maka ita sai shi kuma idan yana nufinka da wani alheri to ba mai mayarda falalansa yana samun wanda yake so daga cikin bayinsa da shi kuma shi ne mai gafara  mai jin kai )
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce (ka kiyaye Allah sai Allah ya kiyayeka ka kiyaye Allah za ka sameshi gaba gareka idan za ka roka ka roki Allah idan za ka nemi taimako ka nemi taimakon Allah ) tirmizine ya rawaito kuma ya ce hadisi hasan sahihi
Daidaituwa akan tafarki mai tsiratar da bayi ita ce take sanya bawa ya zama mai kushuii gaba da girman Allah  ko wace girma ke kankanta gaba da girmansa shi halitta  duk yadda ya kai ga masayi ko duk yadda ya kai ga martabansa ya daukaka to shi halattace ne kuma abin raino ne wanda ake gudanar da shi abin mallaka. Allah Madaukakin Sarki ya ce game da AnnabinSa: (Ka ce ba ni mallaka wa raina wani amfani kuma haka ban tunkude wata cuta face abin da Allah ya so, kuma da na kasance ina sanin gaibi da lalle ne da na yawaita daga alheri kuma cuta ba za ta shafe ni ba.ni ban zama ba face mai gargadi kuma mai bayar da bishara ga mutane wadanda suke yin imani).
Ya kai bawan Allah ka kwadaita daga Allah kuma ka roke shi shi kadai ba shi da abokin tarayya, ya yaye cutarka ya kawo ma amfani ya yaye ma bakin cikinka, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Idan Allah ya shafe ka da wata cuta to babu mai kuranyewa gare ta face shi, kuma idan ya shafe ka da wani alheri to shi ne akan komi mai ikon yi )  kuma Allah mabuwayi mai girma ya ce : (ko wane ne yake karba wa mai bukata  idan ya kira shi kuma ya sanya ku mamayan kasa shin akwai wani abin bautawa tare da Allah?.kadan kwarai kuke yin tuna
lalle babbar manufa na samuwarka -ya kai halitta a wannan rayuwa- shine don ka tsayu bisa tafarkin Allah mikakke akan manhaji wanda yake na rayuwarka da kuma dabi'unka da halayenka a cikin kai-komonka wahayin da aka saukar da shi yayi hukunci akanka da kuma tarihin Annabi wanda aka turo amincin Allah su tabbata agare shi, Allah madaukakin sarki ya ce: (kuma lalle wannan ne tafarkina yana madaidaici sai ku bi shi kuma kada ku bi wasu hanyoyi su rarrabu da ku daga barin hanyata wannan ne Allah yayi muku wasiyya da shi tsammaninku kuna yin takawa )
Ya bawan Allah  ka tsayu bisa ga aiki da alkura'ni mai girma da halaye kan sunnan shugaban annabawa da manzanni zahiri da badini kana mai kuduri kuma kana aiki da shi kana mai hukunci da shi kuma kana mai nema ama hukunci da shi, Allah Ubangiji tsarki da daukaka su tabbata a gare shi ya ce: (kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gareka kuma ka yi hakuri har Allah ya yi hukunci kuma shi ne mafi alherin masu hukunci)
 Allah Mai tsarki da daukaka ya ce :(saboda haka sai ka yi kira kuma ka daidaita kamar yadda aka umarce ka kuma kada ka bi son zuciyarsu kuma ka ce na yi imani da abin da Allah ya saukar na littafi)
Ya kai mumini ka lazimci kiyaye  dokokin Allah kuma ka tsarkake aikinka gareshi shi kadanshi ta hanyan nufatanshi da kuma nema, za ka kasance cikin walwala na har abada  da kuma aminci  cikakke da rabauta mai girma   duniya da lahira za ka zama mafi tsarkakan mutane a rayuwa  kuma za ka kasance mafi cikan ni'ima kuma za ka zama mafi jin dadin rayuwa a cikin mutane da hali mafi dadi Allah madaukakin sarki ya ce :(lalle ne wadanda suka ce Ubangijinmu Allah ne sa'an nan suka daidaitu to babu wani tsoro a kansu kuma ba za su yi bakin ciki ba)(wadannan 'yan Aljanna ne suna madawwama a cikinta a kan sakamako ga abin da suka kasance suna aikatawa )
 Ya wanda ya sarayar da lokutan alheri ya barnatawa kansa ta hanyar aikata zunubai da abubuwa masu halakarwa to ka koma zuwa ga majibincinka Allah ka saurara zuwa ga abin da zai jefa maka fatan alheri a cikin zuciyarka to ka kasa kunnuwarka tare da sauraro daga gareka wanda zai ratsa cikin zuciyarka domin shi din nan kira ne daga wurin Ubangiji wanda ke turo rahamarsa da kaunarsa ga bayinsa, lalle yekuwa ne daga gurin Ubangiji Mai tausayi ga bayinsa duk yanda zunubi ya yi girma munanan laifuka suka daukaka Allah madaukakin sarki yana cewa (ka ce (Allah ya ce) ya ku bayina wadan da suka yi barna akan rayuwarsu kada ku yanke kauna daga rahamar Allah, lalle Allah na gafarta zunubai gabadaya lalle shi, shi ne mai gafara mai jin kai )
sannan ya kwadaitar da bayinSa zuwa ga maida al'amari ga Allah da komawa gare shi kafin tserewan lokaci da sarayar da zamani domin kar a fada cikin hasara da nadama game da sakacin yin da'a ga Allah Mai rahama. Allah Madaukakin sarki yace : (kuma ku mayarda al'mari zuwa ga ubangijinku kuma ku sallama masa a gabanin azaba ta zo muku sa'nan kuwa ba za a taimake ku ba)
(kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga ubangijinku a gabanin azaba ta zo muku bisa auke kuma ku ba ku sani ba)

Huduba ta Biyu
Ya ku bayin Allah ku tsayu kan da'a ga Allah za ku rabauta, ku lazimci koyarwar Alkur'ani da sunna zaku samu walwala, samun daukaka da shugabanci na ga lizimtar addinin Allah da bin sunnar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma kyakkyawan karshe na ga tabbatar da tauhidi da tsoron Allah Mabuwayi abin girmamawa.   
Allah Madaukakin sarki yace : (wadanda suka yi imani kuma basu gauraya imaninsu da zalunci ba wadannan suna da aminci kuma sune shiryayyu)
Kuma kaskanci da walakanci da tabewa da hasara na cikin sabawa Allah da munanan laifuka da sabawa umarni da hani.
 Allah Madaukakin sarki yace : (kuma wanda ya sabawa Allah da ManzonSa kuma ya ketare iyakokinSa zai shigar da shi wuta yana madawwami a cikinta kuma yana da wata azaba mai walakantarwa).