الجمعة، 28 سبتمبر 2018

TABKIN ALKAUSARA


Hudubar Masallacin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi   11-1-1440AH na sheikh Ali Abdurrahman Al-Huzaifi
HUDUBAR FARKO
 DA SUNAN ALLA MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mabuwayi mai yawan kyauta mai gafaran zunubai mai karban tuba , mai tsananin ukuba   ma'abocin yalwa ,  ba abin bautawa da gaskiya sai shi komawa na gare shi  ina  kyautata yabo ga Ubangijina kuma ina gode mishi , ina tuba zuwa gare shi  kuma ina neman gafarar sa, na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya madaukaki mai girma ,  kuma ina shaidawa Annabin mu Muhammadu bawan sa ne kuma Manzon sa  ne ,  mai albishir kuma mai gargadi , ya Allah ka yi dadin tsira  da aminci da albarka bisa ga bawan ka  kuma Manzon ka Muhammad  da iyalan shi da sahabban shi  wanda suka tsere zuwa  ga dukkan falala da alheri   .
BAYAN HAKA: - Ku ji tsoron Allah ta hanyar bin umarninsa  da nisantar abin da ya hana ya tsawatar, ya ku bayin Allah;  ku yi aiki irin ayuka na kwarai domin gyara lahiran ku   kada ku bata ayukan ku sai ku yi hasara wa kanku  Allah madaukakin sarki ya ce (  Ka ce ku yi aiki  Allah zai ga ayukan ku da Manzon sa da muminai sannan a maice ku zuwa ga masanin gaibi da shahada , sai ya baku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa )
     Allah madaukakin sarki ya ce : (Ya ku wadan da suka yi imani ku yi da'a ga Allah ku yi  da'a ga Manzo kar ku bata ayukan ku ).
Kuma Allah madaukakin sarki ya ce : (Lallai hasararru su ne wadanda  suka yi hasarar  kawunan su  da iyalan su ,  ranar alkiyama , wannan shi ne hasara mabayyani )
Ku gyara duniyan ku ta hanyar neman halal da ciyar da  shi cikin kofofin alheri na wajibi da mustahabbi  da kuma  halal , ku sanya wannan duniya din ta zama guzuri a gare ku  zuwa gidan ni'ima   kada  kawa ta duniya ta rude ku  ko  ta fitine ku game da lahira , ka yi aiki ya kai Musulmi domin gyara duniyar ka,   ka yi aiki kuma domin gyara lahirar ka , ya zo a hadisi   ba mafi alherin ku shi ne wanda ya bar lahirar sa don duniyar sa ba  , ko kuma wanda yabar duniyar sa don lahirar sa ba   ,  An karbo daga Mustaurid  dan Sadad Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : (   Mun kasance a wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  muna tuna duniya da lahira  ,  wasun su suka ce  duniya kawai guzuri ne zuwa ga lahira  ,  acikin ta akwai aiki akwai salla ,  akwai zakka , wasu daga cikin su  kuma sai suka ce  lahira a cikin ta akwai aljanna  suka fadi abin da Allah ya so su fada, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :-Misalin duniya in an kwatanta da lahira kamar dayanku ne  ya tafi kogi ya sa yatsarsa ciki ya fitar to ruwan da yatsar ta debon shine duniya,) Hakim ya rawaito a cikin Al Mustadrak, kuma Hakim ya rawaito daga Sa'ad dan Darik daga baban shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:  (Madalla da gidan duniya ga wanda ya yi guzurin lahirar sa daga gare ta  har ya yardar da Ubangijin shi , tir ga wanda ta kange shi daga lahirar sa  ta gajarta mishi samun yardan Ubangijin shi ).

     Hasanul-Basari  Allah ya mishi rahama ya ce : - ( Madalla da gidan duniya ga mumini  sabo da ya yi aiki dan kadan a cikin ta ya karbi  guzurin sa daga gare ta zuwa aljanna,   tir  da gidan  da ta kasance ga munafiki da kafiri sabo da ya sarayar da dararrakin sa sai guzurin sa ta kasance a cikin ta zuwa wuta Ahmad ne ya rawaito a cikin littafin zuhud .
   Kowa ya san dahir cewa shi din nan  mai kaura ne  daga  wannan gidan  kuma ya bar abin da Allah ya bashi anan duniya a bayan shi  ba abin da zai kasance tare da shi sai aikin shi,  in alheri ya yi ya ga alherin sa in kuma sharri ya yi ya ga sharrin sa   to idan har ya kasance halin ko wani daya zai kai ne zuwa ga wannan gayan kuma zai kai ga wannan makomar    , to ya wajaba a gare shi da ya kaddamar da aiki mafi daraja da zai iya yi ga ubangijin shi  na daga cikin ayuka na kwarai  ba wata wasila tsakanin bawa da Ubangijin shi sai da wannan  Allah madaukakin sarki ya ce :- ( Ba wai dukiyan ku ne ba ko 'ya'yan ku  ne suke kusantar da ku zuwa gare mu kusantarwa ba  face wanda ya yi imani ya yi aiki na kwarai to wadancannin ka suna da  sakayya na ribi sabo da abin da suka aikata   alhali kuma suna cikin benayen aljanna  a cikin aminci ).

   Babban damuwar ka ya kai musulmi shi ne ka samu rabauta da sha daga tabkin Annabi  shugaban 'yan Adam tsira da amincin Allah  su tabbata a gare shi , (To yaya za ka cimma wannan manufan?   shi ne farkon abin sha na 'yan aljanna, to duk  wanda Allah ya datar da shi ya mishi baiwan sha daga wannan tafkin  to babu tsoro a gare shi bayan haka , wanda ya kasance  daga cikin wadan da za su zo ga Annabi  su  sha a tafkin Allah zai saukake musu  fitintinun  kafin  haka.
  kuma imani da tafikin imani ne da ranar lahira , wanda bai yi imani da tafkin ba  bai da imani  sabo da rukunnan  imani  ba a rarrabewa tsakanin su to duk wanda ya bar wani rukuni daga cikin rukunnan imani hakika ya kafurce da su  gaba daya .
      Shi Tafki wani kyauta ne daga Allah zuwa ga Annabi sa  Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,    al'umar sa za su sha daga gare shi a kasar da za a tattara al'uma a wurin hisabi ranar alkiyama   a wunin da  mikidarin sa ya kai shekara dubu hamsin ga kafura  Allah zai gajarta shi ga muminai   zai  lullube mutane  a  wannan ranar   awurin hisabi  tare da  bakin ciki  wanda ba za su iyada shi ba ba don Allah ya bawa jikkunan su karfin juriya ba da wanzuwa ba da duk sun mutu gaba daya  kuma zai jarrabe su da kishi  mai tsanani  wanda ke kona hanta a gun tsayawa na hisabi  zai jefa kishi mai tsanani a cikin ciki irin kishin da ba su taba yin irin shi ba ,  Allah zai karrama Annabin sa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da tafki domin al'uman shi su sha daga gare shi , shi kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsaye a gindin tafkin  yana dubi zuwa ga al'umarsa   yana jin dadin haka,  jin dadi mai girma  yana kiran al'umar sa don su sha  ,  fadin tafkin da yalwan sa , hadisai masu  dumbin yawa sun zo wurin bayanin sifar ruwan   da yalwan shi   haka kuma alkur'ani ya zo da ambaton sa a cikin suratul kausar   kuma ko wani Annabi na da tafki , an karbo daga Samarata Allah ya kara yarda a gare shi ( daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce lallai Annabawa za su yi tinkaho a tsakanin su ko wane ne ya fi yawan  mabiya  a cikin al'uman sa to ina fatan ya kasance a wannan ranar na fi su duka  mazowa sha  kuma ko wani  mutum a cikin  su  a wannan ranar yana tsaye a kan tafkin cikakke  yana tare da sanda  yana kiran duk wanda ya sani a  cikin al'umar sa  kuma ko wace al'uma na da alama  wanda Annabin su  zai gane su da ita). Tirmizi da Dabarani suka rawaito.
    Kuma tafkin Annabin mu shi ya fi girma kuma yafi dadi kamar dai shari'arsa   An karbo daga Abu Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce : - daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce : (  Lallai  tafki na ya fi nisan daga garin Aila zuwa Adan  , kuma lallai ya fi nono fari ya fi zuma zaki ya fi kankara sanyi,  kuma  adadin kwanukan shan shi ya fi yawan taurari ) Muslim ne ya rawaito, a wata ruwaya da ba na muslim  ba  ya fi turaren almiski  kamshi.
  An karbo daga Abu Zarri Allah ya kara yarda a gare shi  ya ce:- Daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce :- (Na rantse da wanda rai na yake hanun shi ,; kwanukan shan sa sun fi adadin taurarin da ke sama  da kuma  manyan taurarin ta na sama a cikin dare mai duhu,  kwanon aljanna kuma  wanda ya sha daga gare shi ba zai ji kishi ba har abada  yana  tsatssagowa daga gare shi  indororo guda biyu na aljanna ),  Ahmad ne ya rawaito da Muslim da nasa'i   
An karbo daga Abu Umama Allah ya kara yarda a gare shi daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi  ya ce (Tabki na ya kai kwatankwacin Adan da Amman, ya fi girma kwarai akwai  magudanar ruwa guda biyu :na azurfa da zinari, ruwansa ya fi nono fari, ya fi zaki akan zuma, ya fi turaren Al miski kamshi,duk wanda ya sha daga shi ba zai ji kishi bayan haka, fiskarsa ba zata bakanta ba har abada,) Ahmad da Ibnu Maja da Ibnu Hibban.
An karbo daga zaid bin khalid Allah kara yarda a gare shi, daga Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Shin ko kun san Alkausar? Wani kogi ne da Ubangiji na ya ba ni a Aljanna, yana da alheri mai yawa a cikin shi, Al'uma ta zata sha daga gare shi ranar alkiyama, kwanukan shan sa kamar adadin taurari, zaa fizge bawa daga  gare su sai na ce : ya Ubangiji na ai ya na cikin Al'uma ta sai ace : Ai baka san me ya farar a bayanka ba,) Ahmad ne da Muslim da Abu Da'uda,.
Tafkin  kasa ne mai  fadi, Allah zai cika shi da ruwan Alkausara, yana kwarara a cikin sa Indororo guda biyu na zinari da azurfa  na daga kogin Alkausara, wannan tafkin bai raguwa, kuma kowani mumini da muna zasu sha daga shi, bisa ga kishi mai tsananin gaske, to bayan an sha ba za a ji kishi ba har abada, masu zuwa ga Annabi a tafkin su ne masu bin sunnarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma masu nesatan manyan zunubai, Allah Madaukakin sarki yace : In  kun nesaci manyan zunubai da muka hane ku, zamu kankare muku zunubanku kuma mu shigar da ku mashiga mai girma (Aljanna).
Tare da bin sunnar Annabi suna kira zuwa ga Allah bisa basira, Allah Madaukakin sarki ya ce : (ka ce wannan ne hanya ta ina kira zuwa ga Allah bisa basira ni da wanda ya bi ni, tsarki ya tabbata ga Allah kuma ni ba na cikin masu shirka.)  sai su kira zuwa ga shariar Annabi Muhammad,su nesaci bidia da fararrun abubuwa a  addini, da abubuwan da sharia ta ki na munkari, kuma suna lazimtar Ikhlasi mai kore  riya  da neman aji, da nau'uka na shirka, Allah Madaukakin sarki ya ce : (Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, lallai mun baka Alkausar, ka yi sallah don Ubangika kuma ka yi suka,) Assura
Allah ya sa min Albarka ni da ku a alkur'ani mai girma.
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ma'abocin girma da karramawa,da mulki da ba a samun irin shi, da buwaya wacce babu zalunci,ina kyautata yabo ga Ubangiji na kuma ina gode mishi bisa ni'imtarwa masu yawa,na shaida ba abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke ba shi da abokin tarayya, Mai mulki kuma tsarkakakke, kubutacce daga aibi, na shaida cewa Annabinmu kuma shugabanmu Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne,kuma Manzonsa  ne,tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa da sahabbansa masu daraja, bayan haka ku ji tsoron Allah cancancin tsoronsa, ku yi riko da igiya mai karfi na musulunci,
Ya ku bayin Allah! Abin mamaki da falala irin na wanda Allah ya mar falalar zuwa tabkin Annabi na Alkausara ya sha daga gare shi, ba zai ji kishi ba har abada, kuma abin mamaki da girman hasarar wanda aka hana  shi sha kuma aka kore shi daga gare shi, Ubangijinka bai zaluntar kowa,.
Ya ku Musulmai! Na daga cikin abubuwan da ke hana isa a sha daga wannan tabkin akwai kirkiran bidi'o'i   da farar da abubuwa cikin addini, da kuma yin saddu ga musulunci ta hanyar fadi ko aiki, kamar yadda ya zo a hadisan da aka rawaito kan sababin koran wasu daga cikin wannan al'uma.cikin wadannan hadisan akwai fadin : (Ba ka san me suka farar ba a bayanka,sai manzon Allah ya ce : Nesa daga rahamar Allah ga duk wanda ya canja a baya na, )>
na daga cikin abin da ke hana sha daga tabkin alkausara  akwai manyan zunubai, domin suna kazanta zukata, haka nan riya da son a sani ko son a ji na daga cikin abubuwan da ke hana samun isa ga tabkin alkausara, haka hakkokin wasu da aka zalunta na cikin manyan abubuwan da ke hana samun sha daga tabkin, kuma sakayyar ta yi daidai da aikin ga wanda ya yi lura, domin wanda ya bi shariar Annabi Muhammad a nan duniya ya kuma bi koyarwarsa to zai sha daga tabkinsa, wanda kuma ya sanja ya yi bidia sai ahana shi sabo da saddu da ya yi ga Allah.
Lalle Allah da mal'ikunsa suna salati ga Annabi ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi da aminci tabbatacce.